Manchester United na son dawo da tsohon dan wasan ta Christiano Ronaldo mai shekara 36 a wannan kaka, kamar yadda jaridar Express ta ruwaito.
A bangaren takwara ga United din kuma wato Manchester City, ta nazarin sallamar dan wasan gefenta dan kasar Ingila Raheem Sterling da Benjamin Mendy da kuma Aymeric Laporte don samo dan abin hasafi da za ta dauko Harry Kane da Jack Greelish na Aston Villa.
Yiwuwar komawar mai horas da Tottenham Mauricio Pochetino Ƙungiyar ba lallai ba ne ya ja ra’ayin dan wasan gabanta Harry Kane ya ci gaba da zama a Ƙungiyar, In Ji Jaridar Times.
Pochetino na da aniyar komawa kungiyar, to sai dai ba lallai PSG ta sake shi ba saboda soyayya da take mishi, cewar jaridar Mail.
Ita kuwa jaridar Mirror cewa ta yi Manchester United ta kwallafa ranta kan Kane da kuma Greelish don kara karfafa tsakiyarta da kuma gaba.