Kungiyar Gwamnonin kudu maso gabashin kasar nan sun bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo makasan jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon mai baiwa shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Ahmad Gulak.
Wannan bukata ta fito ne ta bakin shugaban kungiyar kuna gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi jim kadan bayan wata ganawa ta na’ura da gwamnonin suka yi kan lamarin tsaro a Jihar.
Gwamnonin sun ce kinsan Gulak al’amari da ya shafi kasa baki daya, don haka ba abu ne na a zura idanu a yi shiru ba.
“Abun bakin ciki da tashin hankali ne yadda muka samu labarin kisan Ahmad Gulak, wanda wasu marada kishin kansu suka yi” cewar Ƙungiyar.
“Mu a madadin al’ummar yankin kudu maso gabashin kasar nan, muna Allah wadai da wannan mummunar aika-aika, don haka muke kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo wadannan makasa kuma a yi musu hukunci daidai Abinda suka aikata”
Daga bisani gwamnonin sun mika sakon ta’aziyarsu ga iyalan marigayi Gulak, tare da fatan Allah Ya bada dangana.
Idan za a iya tunawa a ranar Lahadi ne wasu da ake kyautata zaton yan kungiyar Inyamurai ta IPOB ne suka hallaka Ahmad Gulak a birnin Owerri na Jihar Imo.