By Ishaq Dabai
Kungiyar masu biredi da samar dashi sun bada wa’adi na ajiye aikin su inda suke zanga zanga a filin taro na nationwide saboda karuwar farashin fulawa da sauran kayan hadin biredi.
Masu samar da burodi sun bada sati biyu matukar komai bai dai daita ba zasu tsunduma yajin aiki a ranar 23 gawatan da muke ciki inda suke ankarar da gwamnatin tarayya halin da ake ciki wanda sukace hakan yana kashe masana’antun samar da burodi.
Shugaban kungiyar na kasa shine ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis yayin gudanar da zaman majalissar zartarwa na kungiyar a Abuja.
Ya kara da cewa tsadar burodi tasamo a saline biyo bayan tsadar da kayan hadin yayi, idan ba’a duba lamarin da wuriba nan bada jimawa ba masu dakon burodi zasu shiga wani hali.
Yace idan gwamnatin tarayya bata fito tayi bayaniba zuwa karewar wa’adin da suka bayar na sati biyu “zamu bawa membobin mu umarnin tafiya yajin aiki na tsawon mako daya.”
Sannan ya koka bisa ga yadda kudin kayayyakin sarrafa burodi yayi tsada inda ya dora alhakin hakan ga harajin da aka sanya musu yayi yawa da hukumar kula da ingancin kayan abinci ta kasa NAFDAC na kudin fito shine ya kara ta’azzara komai.
Comments 1