Bello Matawalle, Karamin Ministan Tsaro, ya ce ’yan kasuwan da ke sayar wa barayi abinci ne ke da alhakin rashin kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.
Mista Matawalle ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Abuja.
Na kira shi kasuwanci domin masu sayar da magunguna na cikinsa, masu sayar da abinci, man fetur da sauran kayan masarufi duk suna cikinsa.
Masu ba da labari suna samun abubuwa da yawa daga yin hakan ana biyansu da yawa akan wannan laifin.
Karanta nanZaben Nijeriya Ya Zama Iya Kudinka Iya Shagalinka-Shehu Sani
Don haka, ba sa son matsalar ta ƙare. mutane da yawa sun shiga cikin kasuwancin in ji shi.
Ya bayyana cewa a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara, ya lura da cewa a lokacin da ake sayar da kwalbar coke a kan naira 100 a birnin Gusau wasu suna sayar da shi a kan kudi har naira 500 ga ‘yan fashi da ke yankunansu.
Haka zalika, idan aka siyar da buhun shinkafa tsakanin N18,000 zuwa N21,000, idan ta isa yankin ‘yan fashin, sai ta kai Naira 80,000 in ji shi.
Ministan, ya kuma ce, tsaro hakki ne na hadin gwiwa ga daukacin ‘yan Najeriya, inda ya bukaci kowa da kowa da su ajiye sabanin da ke tsakaninsu, su hada kai don yakar sa.
Ya ce idan ba don wasu ayyukan da ya yi a matsayinsa na gwamna ba, da yanzu yankin Arewacin kasar nan zamansa ya ci tura.
Idan ba don wasu ayyuka da na yi a lokacin da nake gwamna ba, a wannan lokacin arewacin Najeriya zai shiga cikin wata babbar matsala.
Ku tuna cewa ni ne gwamna na farko a daukacin Arewa, wanda ya katse hanyoyin sadarwa a jiharsa.
Na katse hanyar sadarwar ne domin ba da damar jami’an tsaro su shiga su fatattake wadancan miyagu.
Na yi haka ne saboda akwai lokuta da yawa idan sojojinmu za su yi wasu ayyuka kafin su isa yankin ‘yan fashin sai a sanar da ‘yan fashin.
A wani labarin kumaKa Ji Da Aikin Dake Gabanka,Ka Bar Bata Mani Suna-Matawalle Ga Dauda Lawal
Masu ba da labarinsu za su sanar da su, don haka suka saba yi wa sojojin mu kwanton bauna, suna kashe su.
Don haka, batun tsaro yana da tsauri ayyukan da za mu yi a yanzu shine tabbatar da cewa mun fitar da duk wani mai laifi a kasar nan.
Muna fatan cewa tare da addu’o’in mutane, za mu iya cimma abubuwa da yawa ta hanyar ayyuka da yawa da na san za a yi in ji shi.