Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya tabbatarwa da maziyarta kasar daga kasashen waje cewa za a shawo kan barkewar cutar Ebola a kasar.
BBC ta ruwait cewa, A wani jawabi da ya yi wa yan kasar a ranar Talata, shugaban ya bayyana cewa, ‘yan yawon bude ido na kasashen waje na soketafe tafensu zuwa kasar, tare da, soke tarukan kasa da kasa da aka so gudanarwa a kasar, ko sauya su zuwa wasu kasashe.
KARANTA WANNNA LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Dage Kan Ba Za Ta Biya ASUU Ba ‘Ba Aiki Ba Biya’
Da yake jawabi ga yan kasar, Mista Musuveni ya ce, an gano cutar ne tare da wasu larurori a yankuna shida kawai cikin 146 da ke fadin kasar.
Ya kara da cewa Uganda na zaune lafiya kuma ana maraba da baƙi daga sassan duniya.
Ya kuma ce an bayar da jerin sunayen mutanen da suka kamu da cutar ga hukumomin shige da fice don hana su tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen waje.
Rahotanni sun nuna cewa, An kuma samu wasu mutane 141 da suka kamu da Cutar Eloba yayin da mutane 55 suka mutum tun bayan da aka tabbatar da barkewar cutar a cikin watan Satumba.
Shugaban ya ce an samu ci gaba sosai, wajen shawo kan annobar a fadin kasar ta Uganda.
Kwanaki 18 ba a tabbatar da bullar cutar ba a gundumar Mubende inda abaya barkewar cutar yayi kamari, ko da yake an samu rahoton bullar cutar guda daya a ranar Litinin, a cewar wani jami’an kiwon lafiya.
Mista Museveni ya cigaba da cewa, wasu daga cikin jama’a da ke kin bin ka’idojin kiwon lafiya ne ke kawo cikas ga kokarin shawo kan cutar ta Ebola fadin Uganda.
Mashinan Adedeta Sahu da aka fi sani da boda boda a kasar, na bijirewa dokokin kulle-kulle a yankunan da abin ya shafa tare da jigilar fasinjoji maimakon kaya kawai da aka lamjnce musu.
A gundumar Kassanda kuwa, wasu Mutane 10 yan gida daya ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola.
A Kampala kuma, wasu mutane biyu da ke da alaƙa da zargin kamuwa da cutar ta Ebola sun tsere daga wuraren da aka killace su, zuwa birnin Masaka da kuma birnin Jinja, yayin da dukkansu ake tsammanin sun mutu a can.
Duk da cewa cutar ta bazu zuwa gundumomi masu nisa daga yankin tsakiyar kasar, jami’an Uganda na da kwarin gwiwa cewa za a iya shawo kan barkewar cutar kafin ta yi kamari.
A WANI LABARIN KUMA: Hukumar EFCC Ta Kama Wani Da Ake Zargi Da Canjin Kudade Ba Bisa Ka’ida Ba
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kama wani da ake zargi da canji kudaden ketare ba bisa Ka’ida ba, Mustapha Muhammed wanda aka fi sani da Muaspaha Naira a Abuja.
EFCC ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba sannan ta kuma fitar da hoton wanda ake zargin