Uwargidan tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, Aduke Obasanjo, ta shaida wa mata cewa kada su sa ran mazajensu su za su basu hakuri.
Kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito, ta bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata, a wajen bikin manyan muatne karo na 41 na cocin Celestial Church of Christ International Headquarters da ke yankin Ketu a jihar Legas.
Misis , wacce ta wakilci mijinta a wajen taron, an ruwaito cewa ta shawarci mata kan yadda za su rike gidajensu, sannan ta gargade su da su guji shigar da wasu mutane a cikin lamurorin aurensu.
Ta kuma bukaci mata da kada su raina mazajensu, musamman matan da suke biyan kudi a cikin gudanarwar hakokin iyali, inda ta kara da cewa Allah ya saka musu da alheri.
An jiyo ta tana cewa: “Matan da suke sauke nauyin mazajensu sa’a ne kawai da Allah Ya albarkace su; Don haka bai kamata su raina mazajensu ba.
“Maimakon ace namiji ya yi hakuri, ya kamata mata su koyi yadda za su jagoranci mazajensu zuwa dakin kwana su rika taba su cikin soyayya. Duk abin da kuke yi a gidan zai yi tasiri a kan yara kuma yaran su ne za su taimakemu anan gaba Sauran kulawar da kike yiwa mijinki yana da muhimmanci” inji ta.