Jami’an ‘yan sanda sun kama wani dattijo mai shekaru 50 mai suna Umar Samaila, wanda aka ce shi ne shugaban ‘yan ta’adda a sassan jihar Neja, da kuma Nasarawa da Abuja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Minna, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin a ranar Asabar din da ta gabata bisa la’akari da wasu bayanan da aka samu cewa ‘yan bindiga na shirin yin garkuwa da wasu masu ibada a washegari a wani coci da ke kauyen Buku da ke yankin Abaji a babban birnin tarayya Abuja.
“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne jagoran ruhin addinin ga wasu mashahuran ‘yan bindiga da ke yin katsalandan a jihohin Niger, da birnin tarayya Abuja da Nasarawa,” in ji Abiodun. “A tattaunawarsa ta karshe da ‘yan kungiyar sa a wannan rana, ya umarce su da su cigaba da aikin tare da ba su da tabbacin samun nasara.
“Ya kuma yi alkawarin yin addu’a domin a sako wani dan bindiga da ake zargi mai suna ‘Julli’ a yanzu haka yana hannun ‘yan sanda a Abuja. Za a mika wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Abuja don cigaba da bincike.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kamen Samaila, a cewar Abiodun, ya zo ne kwanaki hudu bayan da jami’an ‘yan sandan da ke yankin Lapai suka kama wasu da ake zargin barayin shanu ne su hudu a wani daji da ke kan iyaka tsakanin jihar Neja da Abuja.
Wadanda aka kama a ranar Talatar makon jiya sun hada da Abubakar Buba mai shekaru 27, da Shehu Jare mai shekaru 20, sai Abubakar Garba mai shekaru 44, da kuma Abubakar Na’Allah mai shekaru 25.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa, ‘yan sandan tare da hadin gwiwar ‘yan banga na yankin sun kwato shanu 40 da tumaki goma sha biyar 15.
“A yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa suna kiwon shanu a cikin dazuzzukan, amma ba za su iya bayar da gamsasshen bayani kan shanun da ke hannunsu ba,” inji shi.
“Ana binciken lamarin yayin da wadan da ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu domin gurfanar da su nan take bayan an kammala bincike.”
Comments 1