• Masu zanga zanga sun toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja.
• “A kawo mana jami’an tsaro ko a bar mu, mu kare kan mu,” inji masu zanga zangar.
• “A tabbatar an bi doka da oda a wurin da lamarin ya sha fa.” Umarnin rundunar yan sandan jihar Kaduna.
Matafiya da dama ne ke tsaye cirko cirko a Kan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja, biyo bayan kulle hanyar da wasu fusatattun mutane suka yi, sanadiyar samun ya waitar hare haren Yan bindinga, musamman ma harin da ya yi sanadiyar mutuwar wata yarinya kyar shekara 13.
Lamarin ya faru ne a Anguwar Magaji dake karamar hukumar Chikun dake jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Mazauna garin sun bayyana cewa, yan bindigan sun afka gidan basaraken kauyen ne, inda suka yi garkuwa da iyalan sa, da wasu mutanan yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: An sake na da Amina Mohammed a matsayin mataimakiyar sakataran majalissar dinkin duniya
Wani mazaunin yankin ya shaida wa majiyar mu cewa, akwai barazanar tsaro a gidajen su, da gonakinsu.
Ya kara da cewa, bama iya zuwa gonakin mu, kuma sukan biyomu har cikin gidajen mu, suyi garkuwa da mu, domin amsan kudin fansan, a cewar sa.
Hakazalika, akwai jami’in tsaro a garin, lokacin da suka kashe yar shekara sha ukun. Sannan sukayi a won gaba da iyalan sarki, da wasu mutanen, Inji shi.
Ya kara da cewa, bukatar al’umar yanki shine, a kawo musu jami’an tsaro ko kuma a bar su, su kare kansu daga hare haren Yan bindingan.
Wani shardan gani da Ido, ya bayyana wa jaridar Daily Trust cewa, masu zanga zangar, sunki sauraran jami’an tsaro, duk da rokon da su kai musu, lokacin da suka zo inda lamarin ke faruwa.
Shaidar wanda ya bukaci a sakaye sunan sa ya ce, masu zanga zangar sun fito hanyar ne tun musalin karfe bakwai da rabi na safe.
A cewar sa, masu zanga zangar na cike da bacin rai lokacin da suka toshe hanyar, inda Ko da jami’an tsaro sukazo, sai mazan suka ja baya, su kabar matayen su a kan hanyar.
Ana sa bangaren jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kaduna ASP Jalige Mohammed ya ce, Kwamishinan yan sandan jihar Umar Muri, ya umarci Kwamandan yan sandan yanki, da ya ziyarci inda lamarin kefaru, kuma ya tabbatar da bin doka da oda.