Mohammed Abdulkadir Isa, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya rasu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Bawan Allah Mai Wa’azi A Kan Hanya Ya Ki Karbar Sadakar Naira 35 Yace Tayi Kadan
Wannan ci gaban ya fito ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ta hannun mai baiwa shugaban majalissar dattawa shawara, Ola Awoniyi.
A cewar sanarwar, Mohammed ya rasu ne a daren Juma’a sakamakon raunin da ya samu a wani hatsarin da ya faru kwanaki biyar da suka wuce.
Sanarwar ta ce: “Tare da mika wuya ga ikon Allah, muna matukar bakin cikin sanar da rasuwar mataimaki na musamman ga shugaban majalisar dattawa kan harkokin yada labarai, Mohammed Abdulkadir Isa.
“Mohammed Isa ya rasu ne a daren Juma’a yayin da ake jinyar raunin da ya samu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi ranar Lahadi a kan hanyar Minna zuwa Suleja a jihar Neja.”
An yi jana’izar gawar mamacin ne da yammacin ranar Juma’a a garin Funtua da ke jihar Katsina kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bokola Saraki da sauran masu ruwa da tsaki na ci gaba da mika sakon ta’aziyya ga tsohon dan takarar shugaban kasa bisa rasuwar mai taimaka masa.
A WANI LABARIN KUMA, Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Sun Bukaci Wani Taimakon Daga Gwamnatin Jiha
Mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a jihar Bayelsa sun koka da halin da suke ciki yayin da suke komawa gidajensu bayan da gwamnatin jihar ta rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar a hukumance.
Gwamnatin jihar Bayelsa ta bude sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin jihar a yayin da ake fama da ambaliyar ruwa a watan jiya. Gwamnati ta kuma samar da abinci da sauran muhimman kayayyaki a sansanonin ga wadanda abin ya shafa.
Amma yayin da ruwan ya fara ja da baya, gwamnatin jihar a hukumance ta rufe sansanonin tare da mayar da mutanen gida, tare da ba wa kowannen su wata alama da za ta taimaka musu na komawa gida ranar Asabar.