Wadansu rahotanni da aka wallafa a shafin Twitter na nuni da cewa Nunuk Nuraini ta rasu. Nunuk wadda ta yi aiki a matsayin manaja a wani kamfani a Indonesia na kusan shekara 30.
Da yawa suna ta yabon ta kan wannan bajinta da ta yi na samar da Taliyar Indomie.
Indomie ta mamaye duka sunayen wata taliya mai irin wannan tsari na ta a Indonesia, inda mutane da yawa suka mayar da ita babban abincinsu na yau da gobe.