Wata dattijuwa a Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin rayuwa bayan da ta shafe sama da shekara 30 dauke da juna biyu.
Wani faifan bidiyo da shafin yanar gizo na Afrimax ya wallafa, ya nuna yadda tsohuwar ke ta karakaina tsakanin cikin gida da kofar gida dauke da katoton ciki da ya wuce misali.
Kamar yadda Datttijuwar mai shekara 72 ta bayyana, ta fahimci sauyi ne watanni shida bayan mutuwar mai gidanta, kuma duk da irin gwaje-gwaje da likitoci suka yi suka tabbatar mata da juna biyun cewa namiji ne, amma har yanzu ba ta samu sauka ba.
To sai dai lamarin ya sauya bayan da ta kara komawa asibiti yayin da ta fara ji sauyi a cikin nata, inda fa likitoci suka bayyana mata cewa a yanzu haka jaririn cikin ya sauya kamanni ya rikide zuwa wani abu daban.
Ko da yake sun shaida mata cewa akwai mafita da za a iya cire abinda ke cikin cikin nata ta hanyar tiyata, to amma kuma zai iya kasancewa kafar ta daya na duniya ne daya kuma a lahira, lamarin da ya razanata ta kasa yarda a yi mata tiyatar.
Tsohuwar wacce ta bayyana cewa dukkanin ƴaƴanta sun rasu, ta kara da cewa makota ne tare da jikokinta ke taimaka da abin sakawa bakin Salati.