Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha (American University), ta ayyana Maidakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Hafsat Ganduje, a masayin Farfesa. Uwargidan Gwamna Gandujen dai, a halin yanzu na koyarwa ne a sashen koyar da ilimi na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK). Wannan jawabin na kunshe ne cikin jawabin Shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, inda aka sanarwa da manema labarai a jihar Kano, a ranar Talatar da ta gabata.
A cewar Shugaban, wata tawaga ce daga Jami’ar wacce Farfesa Muhammad Magaji Rano, ya jagoranta ne suka gabatarwa da Uwargidan Gwamna Ganduje takarda a Fadar Gwamnatin Kano a ranar 15 ga watan Satumban shekarar 2019. Har ila yau, ya ci-gaba da cewa, sauran wakilan sun hada da Farfesa Ibrahim Maigari da Dakta Bala Muhammad Tukur, Darakta Lura da Harkokin Hadin Gwiwa ta Jami’ar.
Da yake gabatar da nasa jawabin, jim kadan bayan gabatar da takardar, Dakta Tukur ya bayyana cewa, matakin bayyana sunan Uwargidan Gwamna Ganduje, bisa wannan sabon mukamin na ta, ya dogara ne, sakamakon yin la’akari da tarihin harkar koyarwar, bincike da kuma gudanar da kyakkyawan nazari ayyukanta a bangaren makarantu.
Sannan ya ce; sun lura kwarai da gaske da matakin Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Ganduje, ya bijiro da shi na batun ilimi kyauta kuma wajibi ga kowa da kowa, tun daga kan matakin Firamare har zuwa na gaba da Sakandire, domin kuwa ko shakka babu zai kara ciyar da harkokin wannan ilimi gaba a dukkanin fadin Jihar Kano, a cewar tasa.
Da take mayar da na ta jawabin, Farfesa Hafsat Ganduje, ta gode wa Shugaban Jami’ar, bisa kokarin samar da wannan Jami’a, tare da jinjina masa bisa jajircewarsa wajen ciyar da yankinsa gaba, sannan ta bukaci al’umma da su yi koyi da wannan kyakkyawan misali na sa.
Har wala yau, Hafsat Ganduje ta kara jinjina wa Farfesa Abubakar Gwarzo, bisa matakin kara samar da irin wannan Jami’a a Kano da kuma Kaduna, sannan ta sake bayyana fatanta na kara samar da irin wadannan makarantu a bangaren Kudancin Kasar nan da makwabtanmu na kasashe masu amfani da harshen Faransanci.