A jiya ne Allah Ya amshi ran Hajiya Jummai Abubakar Tafawa Balewa, wacce mata ce ga Firayiministan Nijeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa.
Iyalan Mamaciyar sun tabbatarwa da majiyarmu cewa hajiya Jummai ta rasu ne a wani asibiti da ke Birnin Ikko.
Ana sa ran a yau za a mayar da ita Bauchi domin jana’iza