• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Sunday, April 2, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Uncategorized

Matasa A Kama Sana’a Don Samun Ingantacciyar Rayuwa

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
April 10, 2019
in Uncategorized
Reading Time: 5 mins read
37 1
0
52
SHARES
472
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Mai karatu barkanmu da war haka, barkanmu da sake saduwa a wannan fili namu mai matukar ilimantarwa. Ga wadanda yau ne suka fara karanta wannan mujallah, da ke tunatar da al’umma game da abubuwan da suka shafi rayuwa, wadanda kuma ake ganin idan aka gyara, to za a samu ci gaba mai amfani.

Har wa yau muna jawo hankalin al’umma wajen gyara tarbiyya da dabi’a ta yau da kullum. A wannan karon muna so ne mu jawo hankalin matasanmu maza da mata game da muhimmancin yin sana’a kowace iri ce, in dai ba ta saba wa dokar Allah ba, ko ba ta saba ka’idojin da gwamnati ta kafa ba. Domin akwai sana’o’in da ba haramun ba ne a Addini, Sana’a ga matasa ta zama wajibi bisa la’akari da halin da ake ciki a duniyarmu ta yau.

Domin ba za a iya cewa gwamnati za ta iya sama wa kowane matashi aikin yi ba, ko da kuwa ya yi karatu zuwa na Digiri ne ko gaba da Digiri, ballantana kuma matasahin da bai samu halartar makaranta ba.

Ita sana’a tana da muhimmanci ko da kuwa a ce mutum ya yi karatun boko ne, domin zai iya zama bai samu aiki ba, ko kuma ya samu aikin, amma saboda halin da a ke ciki a yau, albashin da yake dauka ba ya iya biya masa bukatunsa na yau da kullum.

Domin za ka taras da wani matashin yana da Aure, wasu kuma su ke daukar nauyin iyayensu, sannan kuma ga hidindimun dangi da sauran al’ummar da ke tare da su. Sau da yawa akan yi bayanin matasa, matasa, matasa.

Wannan ya zama wajibi ne bisa la’akari da cewa su matasan ne ginshikin duk wata rayuwa mai dorewa ta al’umma. Don haka idan Allah ya sa matasa suka gyaru, to dukkan al’umma ta gyaru. Saboda haka kuma babu wata hanya ta gyaruwar matashi kamar samun sana’ar dogaro da kai, ta hanyar dogaro da kai ne ake samun matashi natsattse wanda babu ruwansa da shiga duk wani tashin hankali ko aikin da bai dace ba.

Idan matashi yana sana’a, babu yadda za a yi a same shi wajen wasu ayyukan da ba su kamata ba, kamar dai yadda yake a fili cewa duk wani matsahin da aka samu a duk wata hayaniya, to idan aka bincika ba shi da wata takamaimiyar sana’ar da yake cin abinci a ciki, wanda hakan ne ma ke ingiza shi don gudanar da wadannan munanan ayyuka.

Wani lokaci takaici ya kan kamani idan na ga matashi yana zaune babu wani aikin yi, babu zuwa makaranta, babu zuwa koyon sana’a, babu tabuka komai don samun abin daukar nauyin kansa, ballantana na sauran mabukatan da ke tare da shi. Sai ka ga matashi ba ya aikata komai domin kula da rayuwarsa, yana zaune yana sa ido a harkokin mutane.

Irin wadannan matasa da ba su da sana’ar yi sai dai sa ido, wanda Bahaushe ke cewa ‘sa ido sana’ar banza,  to irinsu ne wadanda aka fi saurin amfanai da su wajen aika duk wani nau’i na munanan ayyuka, musamman a wannan lokaci na siyasa, wanda wasu ‘yan siyasa ke amfani da su,  wadanda suka gwammace ma bukatun kansu fiye da na al’umma.

Ina fadin haka ne bisa la’akari da cewa babu wani matashin da zai iya rufe wurin sana’arsa da yake samun riba, ya tafi ya aikata wani abin da ya san zai iya shafar wannan wurin da yake gudanar da wannan sana’ar, ko kuma aikata wani abin da ya san zai hana shi zama lafiya ko al’ummarsa.

Amma idan ya zama ba shi da sana’ar fa, zai zama dan a fasa kowa ya rasa. Sau da yawan na kan wuce wasu wurare, abin takaici sai ka ga matasa sun hada majalisa tun safe har dare babu abin da ake yi a wannan majalisa sai gardandami da sa ido akan masu wucewa ana gulmarsu, inda wasu ma a irin wannan majalisar ce ake kitsa wasu munanan abubuwan, kamar shirya zuwa sace-sace ko sare-sare ko wani nau’i na badala.

A irin wannan ne kuma ake samun irin matasan nan masu fatan Allah kawo tashin hankali, ba don komai ba, sai don kawai su samu yanayin tare mutanen da ba addininsu daya ba, su kashe su sace masu kudade da sauran kaya masu amfani da ke jikinsu.

Za ka taras da wadannan matasa suna da mautukar bukatuwa ga abubuwa na rayuwa, manyan wayoyin hannu, sutura mai tsada, neman mata, a wasu ma za ka taras har da shaye-shaye.

To idan babu kudaden da za a yi wadannan abubuwa, babu tunanin da matashi zai yi illa shiga duk hanyar da zai shiga don samun kudaden da zai biya wa kansa bukata, ga shi kuma ya ki kama sana’a.

Sai dai duk da wadannan abubuwa da nake fada, ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai matasan da suka dukufa wajen neman na kansu, wadanda suke gudanar da sana’o’insu, wasu ma har suna koya ma wasu zaka ga suna yi. Kuma Su ke daukar nauyin kansu, na iyalansu da ma na iyayensu.

A irin wannan na ga wani matasahi a Rigasa ta Kaduna, mai suna Muhammadu, wanda ya fita daban da saura matasa. Shi wannan matashi mutum ne mai hannu daya, sannan daya hannun ma a tauye yake, yatsu biyu ne kawai ke amfani a hannun nasa, amma wannan bawan Allah shago yake da shi inda ake cajin wayar salula, kuma yana sayar da katin waya.

Wani abin sha’awa ga wannan matashi shi ne, da hannu dayan nasa yake zuwa ya bude shago ya karbi wayoyin mutane ya yi masu caji, da hannun dayan ne yake gyaran jannaretan da yake amfani da shi. Yana da iyaye, yana da mata har da ’ya’ya.

Don haka ya za ka hada wannan bawan Allah da matashin da yake lafiyayye, amma ya kafa daba ya zauna a majalisa ana musu da shi? Sannan kuma duk da wadannan matsaloli, kamar yadda na ce ba a taru an zama daya ba, akwai matasa da dama da suka dukufa wajen neman na kansu.

Wasu ma su ke daukar nauyin kansu a makarantu, ta yadda za ka tarar da matashi ne ke daukar nauyin kansa tun daga Sakandare har zuwa Jami’a, domin wasu idan da don ta iyayensu ne, to da ba za su yi karatun ba. Haka kuma ko a gwamnatoci ma, akan tarar da wasu gwamnatocin sun dukufa wajen koyar da sana’o’in hannu ga matasa ta yadda za a su samu abin dogaro da kai, musamman ganin irin rawar da suke takawa a duk wata harka ta tsaro ko ci gaban al’umma ko akasin haka.

Haka kuma baya ga gwamnati, wasu ’yan siyasar ma sukan gudanar da irin wadannan abubuwa, ta yadda za ka tarar da wani dan siyasa, dan majalisar dokoki ko na tarayya ko wani mashawarci na Gwamna ko Shugaba kasa ya ware dan wani abu daga cikin abin da yake samu, yana daukar nauyin wasu matasa wajen koya masu sana’o’i.

Wannan abin a yaba ne, ina ma a ce kowane dan siyasa yana yi  haka! Da wannan ne nake kira ga matasanmu su dage wajen ganin sun sami wata sana’ar da za su rinka yi suna samun abin da za su rinka daukar nauyin harkokinsu na yau da kullum.

Su rungumi harkar sana’a komi kankancinta, domin ta haka ne za su zama manyan gobe managarta, wadanda sun fi karfin wani mara kishin su ya yi amfani da su wajen aikata munanan ayyuka. Ya zama kowa yana da sana’arsa, ta yadda matashi ko da yana karatun Jami’a ne, to ya zama idan ya samu hutu akwai inda zai je ya yi sana’a, ballantana kuma a ce ba ya zuwa makaranta.

Domin ita harka ta makaranta ba kowa ba ne ke da dama ko halin samun zuwa, amma sana’a afa? Kowa yana da hali da daman zuwa, matukar Allah ya ba shi lafiya. Sannan kuma, kamar yadda na fada a sama, yana da kyau gwamnatocin tarayya, jihohi da Kananan Hukumomi da saura ’ya siyasa su fito da hanyoyin da za su rinka koya ma matasa sana’o’in hannu ta yadda za su samu abin dogaro da kansu. Domin matasa ne ginshikin kowace al’umma.

Tags: matasamu daina zaman banzamu nemi na kanmusana'azaman banza
Previous Post

Wajibi ne mu Himmatu wajen kare Hakkin ‘ya’ya Mata a Najeriya

Next Post

WASU ‘YAN SA KAI SU 500 SUN SHIGA DAJI NEMAN ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA.

Next Post

WASU 'YAN SA KAI SU 500 SUN SHIGA DAJI NEMAN 'YAN TA'ADDA A JIHAR KATSINA.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
Arabic Arabic English English French French Hausa Hausa
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2507 shares
    Share 1003 Tweet 627
  • Batun Dakatar Da Opay Da Palmpay, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance

    2279 shares
    Share 912 Tweet 570
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    2051 shares
    Share 820 Tweet 513
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1766 shares
    Share 706 Tweet 442
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1390 shares
    Share 556 Tweet 348
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023
NCC Na Shirin Samar Da Cibiyoyin Neman Taimakon Gaggawa

NCC Na Shirin Samar Da Cibiyoyin Neman Taimakon Gaggawa

April 2, 2023
Ukraine Tayi Tir Da Sabon Muƙamin Rasha A Kwamitin Tsaro na MDD

Ukraine Tayi Tir Da Sabon Muƙamin Rasha A Kwamitin Tsaro na MDD

April 2, 2023
Ku Shirya Barin Gidan Gwamnati – ADC ta Fadawa Gwamnan APC

Ku Shirya Barin Gidan Gwamnati – ADC ta Fadawa Gwamnan APC

April 1, 2023
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus
Labarai

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba
Labarai

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8
Labarai

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus
  • Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba
  • Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In