A sanyin safiyar yau Litinin, Matasa masu yawan gaske sun je majalisar dokokin jihar Filato domin nuna adawa da tsige tsohon kakakin majalisar jihar, Hon. Abok Ayuba Nuhu.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, tun da musalin karfe 4 na safe matasan suka fara turuwa a harabar majalissar.
A ranar Alhamis ne aka tsige Abok tare da maye gurbinsa da Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pengana ta karamar hukumar Bassa dake jihar.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Naanlong Daniel, wanda ya jagoranci tsigewar ya yi ikirarin cewa, 16 daga cikin 24 na majalisar ne suka sanya hannu kan tsige Tsohon Shugaban majalissar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun hallaka Wani Fasto a Jihar Delta
Sai dai Abok ya musanta adadin wadanda suka goyi bayan tsige shi, inda ya kara da cewa tsige shi ya sabawa doka, domin kashi 2/3 na mambobin ba su sanya hannu kan tsige shi ba.
Jim kadan bayan tsige shi a ranar Alhamis din da ta gabata, kakakin majalisar ya yi Wata ganawa tare da mambobin da ke masa biyayya a unguwar Zawan a karamar hukumar Bassa ta jihar.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, duk da kasancewar jami’an tsaro a kewayen harabar majalisar, wasu fusatattun matasa sun je majalisar domin nuna adawa da tsige tsohon kakakin majalisar.