An kashe wani fasto mai suna Sylvester Yerinbide na Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) a yankin Aladja da ke karamar hukumar Udu ta jihar Delta.
Ya fito ne daga makwabciyar garin Ogbe-Ijoh a karamar hukumar Warri ta Kudu maso Yamma dake jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kai wa Yerinbide hari a daren Juma’a, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa unguwar Aladja.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu tuka babur a garin Ogbe-Ijoh ne suka gano shi, inda suka garzaya da shi asibiti a unguwar domin yi masa magani, Amma daga bisani ya rasa ransa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin da yasa na Ziyarci Buhari~ Inji Tunibu
Kungiyar matasan Ijaw (IYC) da ke Ogbe-Ijoh ta yi ikirarin cewa maharan sun fito ne daga al’ummar Aladja.
Shugaban al’ummar Aladja, Elder Otto Ogbiruveta ya musanta ikirarin, yana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike na cikin gida domin kama wadanda suka aikata kisan.
Kazalika Idan za’a iya tunawa, Al’ummomin biyu sun yi arangama a baya amma gwamnatin jihar ta samar da zaman lafiya kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta Bright Edafe ya ce har yanzu rundunar ba ta san da faruwar lamarin ba.
Comments 2