Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya kalubalanci matasan Najeriya kan baccin da suka yi, inda ya bukace su da su tashi su karbi ragamar shugabancin kasar maimakon jiran gaba.
Obasanjo ya bayyana haka ne a jiya Asabar, a yayin wata tattaunawa ta musamman da tsohon dan wasan Super Eagles, Segun Odegbami, a gidan filinsa na Eagle7 Sports a Abeokuta, jihar Ogun.
Zargin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan gaza ganin wani matashin shugaban kasa gabanin zaben shekara mai zuwa.
Obasanjo ya nanata cewa ya kamata matasa su yi watsi da lakabin “shugabannin gobe,” yana mai cewa gobe ba za ta taba zuwa ba.
Tsohon shugaban kasar ya ce wasu gurbatattun shugabanni za su ruguza abin da ake kira gobe idan matasa suka kasa tashi tsaye wajen daukar makomarsu a hannunsu.
“Shawarata ga matasan Najeriya ita ce kada su bari wani ya gaya musu cewa ku ne shugabannin gobe.
Idan kun jira gobe kafin ku karbi ragamar shugabancin, to gobe ba za ta zo ba. Za su halaka shi.
“Wannan shine lokacin da ya kamata matasa su tashi su tabbatar da hakan,” in ji Obasanjo yayin da yake amsa tambayoyin Odegbami.
Da aka tambaye shi ya bayyana irin soyayyar da yake yi da noma, Obasanjo ya ce abin da bai yi kwatsam ba a duk rayuwarsa shi ne noma.