Wata ‘yar Najeriya ta bayyana wa soshiyal midiya halin da ta ke ciki inda ta ce ta na nema wa tsohon saurayinta mafita saboda halin da ya tsinci kansa, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda ta wallafa labarin tare da sakaya sunanta a wani rukuni da ke Facebook, ta shaida cewa matashin asali dan asalin Akwa Ibom ne, kuma shekaru 15 da suka gabata.
KU KARANTA: Adeleke zai binciki Oyedelo kan bashin biliyan 407
Ta je hutu gidan antinta inda ta hadu da matashin wanda makwabcinsu ne. A lokacin tana shekarar farko a jami’a, sai suka fara soyayya.
Ta bayyana cewa bayan ya dirka mata ciki sai ya musanta cewa shi ne ya yi mata, har yana barazanar da hukuma ta kama ta.
A cewarta lamarin ya yi matukar ba ta mamaki. Daga bisani dai ta je kemis inda aka zubar mata da cikin. A nan ne ta dinga tsine masa kan yadda ya juya mata baya.
Ta ce ta yi kuka da jikinta inda ta bukaci Ubangiji ya yi mata sakayya ya kuma ci gaba da rayuwarta. Ta ce da ya nemi yafiyarta za ta yafe masa amma ko kadan bai sake bin ta kan ta ba.
Saidai matar ta ce bata ji dadin yanayin da ta gan shi ba saboda ita har ta yi aure ta hayayyafa. A cewarta, farkon 2022 ta gan shi yadda ya tsufa duk ya lalace, bai yi aure ba balle ya haihu.
Ya ce ya sanar da ita cewa an ce masa abinda ya yi mata ne ya janyo masa wannan gagarumar matsalar in da ya roki gafararta. Ta ce ta yafe masa bayan ganin halin da ya ke ciki.
Dole ciki ya sadudar da ke: Hotunan yadda halittar wata mata sauya bayan ta samu juna biyu
Wata mata ta wallafa bidiyonta kan yadda halittarta ta sauya gabadaya sakamakon yadda ta samu juna biyu, Legit.ng ta ruwaito.
Matar mai suna Haeyosato ta wallafa bidiyon ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Disamba, inda nan da nan ta samu adadin kallo miliyan 7.5.