Ƴar takarar kujerar majalisar dokoki ta mazaɓar Owode/Onire, a ƙaramar hukumar Asa ta jihar Ƙwara, Rukayat Motunrayo, ta lashe zaɓen.
Rukayat Motunrayo tayi takara ne ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Rahoton jaridar Daily Trust
KU KARANTA KUMA: Dikko Radda Na Gab Da Lashe Kujerar Gwamnan Jihar Katsina
Da yake sanar da sakamakon zaɓen, baturen zaɓe na ƙaramar hukumar, Farfesa Akeem Olasunkanmi Ijaiya, ya bayyana cewa ƴar takarar ta samu ƙuri’u, 7,521 inda ta lallasa abokin hamayyar ta na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Abdullahi Magaji, wanda ya samu ƙuri’u 6,957.
Ƴar takarar itace ƴar majalisa mafi ƙarancin a jihar sannan wacce ta iya yiwuwa itace mai mafi ƙarancin shekaru cikin ƴan majalisar dokoki na jihohi da suka samu nasara a faɗin ƙasar nan a zaɓen 2023.
Bayyana nasarar ta ya sanya mutane sun fara murna a mazaɓar inda suka fito kan tituna domin murnar lashe zaɓen.
Da take magana kan nasarar da ra samu, ƴar takarar nuna godiyar ta ga mutanen da suka fito suka kaɗa mata ƙuri’a.
“Ina miƙa godiya ta ga mutanen mazaɓata da suka fito kwan su da ƙwarƙwatar su suka zaɓe ni.” Inji ta
Gwamna Makinde Ya Tika Folarin Na APC Da Kasa Ya Lashe Zaben Gwamna
An ayyana gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Oyo da aka gudanar ranar Asabar.
Makinde wanda dan takarar jam’iyyar PDP ne ya doke Teslim Folarin na jam’iyyar APC da Adebayo Adelabu na jam’iyyar Accord inda ya lashe zaben.