Ƙungiyoyin addini a jihar Kaduna sun fito da hanyoyin warware abubuwan da ke sabbaba hare-hare a yankin sakamakon ci gaba da tashin hankali da ake fama da shi a kudancin jihar.
Majalissar da ta kira taron manema labaru don nuna damuwa game da rashin zaman lafiya a kudancin Kaduna ta ce matuƙar gwamnati ba za ta hukunta masu laifi ba, to rikici ba zai kare ba.
A cikin wata hira da Malam Abdurrahman Hassan, sakataren majalisar ta kolin ya bayyana cewa, gwamnati ta kakkafa kwamitoci a lokutan baya da nufin neman hanyar shawo kan matsalar sai dai rashin aiwatar da shawarwarin kwamitin ne sanadin ci gaba da tashin hankali domin ba a hukunta waɗansu ba ya zama ishara ga masu neman tada fitina.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-hallaka-mutum-33-a-zangon-katat-na-jihar-kaduna
A nata ɓangaren, ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya wato CAN tana da ra’ayin cewa matsala ce ta cikin gida dake buƙatar al-ummar yankin su zauna su tattauna. shugaban ƙungiyar CAN a jahohi sha tara na Arewacin Najeriya Reverend Yakubu Pam ya ce an jima ana fama da rikicin sabosa da haka al’ummar yankin ya kamata su zauna su tattauna, su fahimci juna.
Ada dai hare-haren ‘yan-bindiga sun addabi al-umar yankunan Kerawa, Giwa, Birnin Gwari kawai a jahar Kaduna kafin daga bisani kuma suka koma yankin kudancin Kaduna inda aka hallaka mutane da kuma jikkata wasu da dama.