Kakakin majalisar Nijeriya, Femi Gbajabiamila, ya kai ziyara jihar Katsina domin duba yanayin rashin tsaro a jihar domin bankado hanyoyin da za a magance su.
Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Katsina a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar, Aminu Masari. Ya ce sun zo Katsina ne domin su ga me ke wakana, kuma mene ne a kasa domin tattaunawa da gwamnan domin bankado hanyoyin da za a bi a magance matsalar tsaron.
Ya tabbatar da cewa Nijeriya kasa daya ce, jiha kawai ba za ta iya magance matsalar tsaron ba, sai an hada hannu guda wajen magance matsalar.
“Mun kasance a Zamfara da Borno, duk yanayin iri daya ne, duk inda ka je.” In ji shi. Ya ce zancen garkuwa da jama’a shi ya fi ta’azzara a Katsina duk da dai yanzu a cewarsa abubuwan da sauki saboda yadda gwamna ya tashi tsaye wajen magance matsalar.
Masari da yake maida bayani, ya ce; yanayin barin iyakar Nijeriya a bude ya taimaka wajen matsalar tsaro a kasar.