Wata kungiyar mai zaman kanta, NEDF ta nemi ‘yan Nijeriya da su taya jami’an tsaron ‘yan sandan Nijeriya da addu’a da kuma ba su hadin kai tare da sauran hukumomin tsaro wajen aikin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar.
Taju Dolapo, shugaban kungiyar NEDF, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja. Inda ya ce tuni suka kirkiri #PRAYFORPOLICE domin taya ‘yan sandan da addu’a.
Dolopo ya ce ‘yan sandan Nijeriya suna da bukatar goyon baya, bayanai daga ‘yan Nijeriya, da kuma kayan aiki wanda zai taimaka musu wajen tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya.