Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya soki shugabbanin tsaro bisa yadda suke aiwatar da ayyukansu, ganin yadda ake ta kai hare-hare a arewacin Najeriya.
A cewar shugaban, dole sai an kara kokarin da ake yi wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a kasar nan.
Babban mai bai wa Buhari shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno ne ya bayyana kalaman shugaban jim kadan bayan da Buhari ya gana da shugabbanin tsaron a jiya Alhamis.
Wadannan kalaman na shugaba Buhari sun kasance kalamai mafiya kaushi game da salon shugabbanin na tsaro a arewacin Najeriya, a daidai lokacin da yanayin tsaro ke kara ta’azzara.
A cewar Mongonu shugaban kasa ya nuna matukar damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara muni a kasar nan.
“Shugaban kasa yana ganin duk da cewar hukumomin tsaro na kokari, kokarin nasu bai isa ba wajen cimma burinsu cikin gaggawa,” a cewar Mongonu.