A yanzu haka dai da yawa daga cikin matuka keken Napep na gudanar da zanga-zanga a unguwar Abule-Egba da ke jihar Legas bisa zargin kashe daya daga cikinsu da wani dan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na Meran ya yi.
Ma’aikatan sun fito kan titi ne a safiyar ranar Alhamis, inda suka tare duk hanyoyin shiga da fita na Meran, dake garin Abule-Egba, domin nuna rashin jin dadinsu kan kashe-kashen da ‘yan sanda ke yi a baya-bayan nan.
Wasu dai sun ce dan sandan ya caka ma wani matukin Keke Napep wuka ne, yayin da wasu kuma suka ce dan sandan ya harbe shi har ya mutu a gefen titi.
An gano cewa lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis a kan titin Command, Meran, Abule-Egba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Alkaliman Wadanda Suka Mutu a Legas ya karu daga 22 Zuwa 36
Hankali ya tashi yayin da rahotanni ke cewa masu tuka Keke Napep din, na shirin mayar da martani ta hanyar kai wa ofishin ‘yan sanda hari.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, wanda ya tabbatar da zanga-zangar ta hanyar sakon WhatsApp, ya ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya tura ‘yan sanda yankin domin kwantar da hankulan al’uma da kuma tabbatar da oka da Oda.