Kwamitin wucin gadi na majalisar dattijai mai kula da rashin daidaiton rabon asusun raya kasa na Naira biliyan 500 da bankin raya kasa na Najeriya (DBN) ya zayyana hukunce-hukuncen aiwatar da shirin zuba jarin jin dadin jama’a da ministar harkokin jin kai, da Hajiya Sadiya Umar Farouq ta kaddamar.
Ministar tare da tawagarta sun mutunta gayyatar kwamitin binciken ne a ranar Litinin din nan, amma ta kasa baiwa kwamitin tabbatacciyar shaida ta wadanda suka ci gajiyar shirin NSIP.
KU KARANTA: Italiya: Yan Sanda Sun Kama Wani Yana Tuƙa Mota Ferari Ta Bogi
Kwamitin wanda Sanata Sani Musa ya jagoranta, ya gabatar da tambayoyi kan ayyukan hukumar da suka shafi shirin zuba jari na kasa (NSIP) wanda ministar ta kare kanta ba tare da tantancewa ba.
Ta ce: “Kimanin dalibai miliyan 9.8 a fadin kasar nan tuni suka fara cin gajiyar shirin ciyar da makarantu a kan kudi naira 100 a kowane abinci, baya ga wadanda suka ci gajiyar shirin.”
Sai dai shugaban kwamitin da sauran mambobi kamar Ayo Akinyekure, Uche Ekwunife da Mathew Urhoghide sun shaida wa ministar cewa abinda ta gabatar sun yi kyau a takarda amma ba su da komai na rikewa da sunan amfani.
‘Yan majalisar sun yi wa ministar salon ba ruwan mu, yayin da Sanata Ayo Akinyelure ya bayyana cewa duk kudaden da gwamnatin tarayya ta yi amfani da su a cikin shirin sun bace a iska, duk da cewa babu alamar NSIP a yankin Ondo ta tsakiya da yake wakilta.
Don haka, kwamitin ya umarce ta da ta gabatar da sunayen wadanda suka ci gajiyar shirin daban-daban, adireshinsu da lambobin wayarsu a kan jihohi, kananan hukumomi da kuma gundumomi a cikin mako guda.
A wani labarin kuma: Kasashen G7 Sun Dauki Wani Mummunan Mataki Kan Rasha
Farsashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwannin duniya , bayan manyan masu fitar da ɗanye mai sun amince su ci gaba da rage yawan man da suke fitarwa , yayin da ƙungiyar ƙasashe 7 masu ƙarfi tattalin arziki wato G7 da ƙawayensu su kace zasu rage farashin manfetur ɗin ƙasar Rasha.
Farashin ɗanyen mai ya ƙaru da kashi 0.6 inda a yau Litinin da safe farashin Ganga ɗaya ya kai Dalar Amurka 86.