Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce kalaman Ministocin Ilimi Adamu Adamu da na Kwadago da tabbatar da nagartar aiki, Chris Ngige, wani yunkuri ne na gwamnatin tarayya na ruguza jami’o’in gwamnati.
Majiyar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Kungiyar ta kuma yi zargin cewa mugun nufin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na hana matasan Najeriya samun ingantaccen ilimin jami’a a yanzu ya fito fili.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) sun ce sun dakatar da yajin aikin na tsawon watanni 8 bisa bin umarnin kotu a matsayin kungiyar ta masu hankali da bin doka da oda.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, (KUST) a jihar Kano shugaban kungiyar malaman jami’o’i, shugaba da sakatare, Muhammad Sani Gaya da Murtala Muhammad, suka fitar tare da sanya hannun hadin gwiwa a ranar Alhamis.
KU KARANTA KUMA Gwamnatin Tarayya Ta Dage kan Baza ta biya ASUU Albashin su ba
Sanarwar ta ce matakin hana albashin watanni bakwai (7) da biyan rabin albashin watan Oktoba, wata shaida ce ta kokarin gwamnatin tarayya na kawo karshen ingantaccen ilimin jami’a.
Kungiyar ta ce gwamnatin tarayya za ta so a tunatar da cewa malaman jami’o’in Kasar nan ba ma’aikatan wucin gadi ba ne.
Sanarwar ta kara da cewa, ”Abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya a karkashin gwamnatin Manjo Janar Muhammad Buhari (mai ritaya) ta yanke shawarar hana mambobinmu albashin watanni bakwai tare da biyan rabin albashin watan Oktobar 2022.
‘’Wannan shawarar ba ta da tushe balle makama da kuma nuna jahilcin gwamnati game da alhakin ma’aikatan ilimi ko kuma cin zarafin ofishin. An bayyana ayyukan a fili a cikin dokokin da suka kafa jami’o’i, waɗanda ke da sauƙin tantancewa.”
A cewar sanarwar, ”Kamar yadda a yau, Najeriya ta zama ta uku (3) a Afirka mafi yawan takardu a cikin bayanan Scopus kamar yadda aka nuna a cikin Scimago (https://www.scimagojr.com) saboda yawan abubuwan bincike.
A Wani Labarin Kuma 2023: Babban Sufetan Yan Sanda Ya Zargi Gwamnoni Kan Rikice-rikicen Siyasa
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasar nan, Mista Usman Baba, ya dora alhakin karuwar rikice-rikicen siyasa da ake samu a kasar kan wasu gwamnonin jihohi.
Baba ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis din nan a Abuja.