Muƙaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (Ag. CGI), Isah Jere Idris ya yi wani gagarumin yunƙuri don biyan ɗimbin bashin takardun fasfo a Ofishin Fasfo na Ikoyi da ke Legas ta hanyar tura tawaga ta musamman.
Muƙaddashin CGI ɗin ya ɗauki matakin ne bayan ya samu rahotanni game da jinkirin da wasu masu neman fasfo ke samu game da fasfunansu a ofishin na Ikoyi a Legas.
ACI Amos Okpu, Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai, indaya ce tuni tawagar ta isa Ikoyi Legas kuma ta fara aikin biyan bashin don tabbatar da cewa an kammala duk wasu aikace -aikacen Fasfon a cikin mako.
Idan za a iya tunawa, lokacin da ya hau kan muƙamin, muƙaddashin Kwanturola Janar Idris Isah Jere ya yi alƙawarin ƙarfafa sake fasalin bayar da Fasfo don tabbatar da ayyukan bayar da Fasfon na tafiya ba tare da matsala ba a dukkan cibiyoyin bayarwa.
“Muƙaddashin Kwanturola Janar yana son yin amfani da wannan damar don tabbatar wa masu neman Fasfo da suka yi rajista a Ikoyi Legas cewa tawagar za ta fara bayar da sanarwa ga masu Fasfo ɗin don su je su karɓa, don haka su kasance cikin shiri. Ya ba da tabbacin cewa za a yi wasu manyan canje -canje a ofishin don inganta ayyukan fasfons. ” A cewar sanarwar.
A halin yanzu, muƙaddashin Kwanturola Janar yana ƙara kira ga masu neman Fasfot da su yi ƙoƙarin ziyartar shafin intanet na hukumar a adireshin: immigration.gov.ng don neman fasfo da biyan kuɗaɗen duk nau’ikan da suke so kuma su guji hulɗa da ‘yan bayan fage da ke neman su biya tsabar kuɗi a hannu.