Mutane 5 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kyegegwa zuwa Mubende a ranar Asabar.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan Rwenzori West, Vincent Twesige, hatsarin ya afkune tsakanin wata mota kirar Toyota Hiace ‘drone’ mai lamba UBF 534N da kuma mota kirar Toyota Hilux Mai lamba Reg no. UAY 052Z, .
Mota Kiran ‘Drone’ na kan hanyarta ce na zuwa Kampala daga Kasese a lokacin da ta yi karo da motar daukar kaya biyu da ta taso daga Kampala zuwa Bwera. Mutane biyar da ke cikin motocin suka mutu nan take.
Wadanda suka mutun an bayyana sunayensu kamar haka; Amidu Kawuntura, Kagimu, da Assira Caroline Prima, yayin da ba a tantance sunayen mutane biyu da abin ya shafa ba.
An garzaya da wasu fasinjoji takwas da suka samu munanan raunuka zuwa cibiyar kula da kiwon lafiya ta Kyegegwa IV domin yi musu magani.
‘Yan sanda sun ce an kai gawarwakin wadanda suka mutun zuwa Asibitin na Kyegegwa IV, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin hadarin.
Kazalika Kakakin Rundunar Yan sandan ya ja kunnen jama’a game da tukin ganganci gabanin bukukuwan karshen shekara.
Comments 1