Akalla fararen hula 22 ne aka kashe a ranar Lahadin da ta gabata a wani harin da ‘yan tawaye suka kai a arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Kafafen yada labaran kasar sun rawaito cewa kungiyar hadin gwiwar ci gaban Congo CODECO ce ta kai harin kan sansanin ‘yan gudun hijira na Ivo da ke jihar Ituri.
Yan kungiyar dauke da makamai sun bude wuta kan masu neman mafakar inda mutane da dama suka tsere daga sansanin.
A makon da ya gabata ma wani hari da aka kai a sansanin ya yi sanadin mutuwar fararen hula 29.
Shugaban kasar Felix Tshisekedi ya ayyana harin da sojoji suka kai a jihohin Arewacin Kivu da Ituri a ranar 7 ga watan Mayu domin tabbatar da tsaro sakamakon karuwar tashe-tashen hankula.
An sallami jami’an kula da farar hula na yankin tare da maye gurbinsu da jami’an soji a wani bangare na samar da tsaro.
Tsawon shekaru kusan 20 ne kungiyoyin da ke dauke da makamai ke kokarin sarrafa Zinare da Cobalt da sauran ma’adanai a yankin ta hanyar kai hare-hare da fadace-fadace a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango mai iyaka da kasashen Rwanda da Uganda da kuma Burundi.