Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin gwamna Masari ta bai wa ‘yan bindigar jihar wa’adin Awa 48 da su tattara yana su yana su su bar jihar ko su fuskanci mummunan fushin gwamnati akan su.
Masari ya ce ya bai wa ‘yan bindigar da ba su tuba ba wannan wa’adin kafin hukuma ta zo kansu.
Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Muhammad Inuwa shi ne ya bayyana hakan a yayin da yake yiwa manema labarai bayani a gidan gwamnati dangane da matakin da gwamnati za ta dauka dangane da ‘yan bindigar da ba su tuba.
Sakataren gwamnatin ya ce gwamnan ya dauki wannan matakin ne bayan zaman da ya gudana tsakanin gwamnatinsa da Kwamandan runduna ta 8 ta Sakkwato, Janaral Aminu Bande, da wadansu kuma tubabbun ‘yan bindigar daga jihar Katsina da Zamfara.
Inuwa ya ce yanzu gwamnati ba za ta sake ta dauki kaskanci daga ‘yan bindigar ba wajen karya doka da tada zaune tsaye a jihar.