Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta bayyana cewa, sun fi fuskanci matsaloli da dama daga masu jefa kuri’a da kuma harkar zabe a jihar Kogi fiye da abin da suka fuskanta a jihar Bayelsa.
An gudanar da zaben gwamnoni a jihohin biyu, amma an kuma gudanar da zaven kujerar Sanata a mazabar Kogi ta Yamma.
Bayanai sun nuna cewa, an yi amfani da kudade a jihohin biyu, an kuma samu tashin hankula a dukkan jihohin, amma abin da ya faru a jihar Kogi na daban ne.
Amma a jawabinsa a gidan talabijin na Channels da yammacin ranar Asabar, jami’in watsa labaran rundunar ‘yan sanda, Mista Frank Mba, ya ce, hukumar ta samu rahotannin tashin hankula a jihar Kogi fiye da abin da ya faru a jihar Bayelsa, ya kuma dora laifin rikincin a kan ‘yan siyasa, yana mai cewa, yan sanda sun yi iyakan kokarinsu.