Yan uwa da abokan arziki na daliban nazarin gandun daji dake Afaka na Jihar Kaduna na ci gaba da murna baki har kunne bayan sakin daliban 27 da yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Yayin da suka hallara a harabar Makarantar a jiya, yan uwa da iyayensu na ta zubar da hawayen farin ciki, yayin da dalibai yan uwansu ke ta wakokin mubaya’a bayan shafe kwanaki hamsin da shida hannun mugayen yan bindigar.
A hannu guda daliban wadanda suka shiga halin dimuwa da firgici hannun yan bindigar, sun yi ta bayyana farin ciki da jin dadi, ko da yake a bangare guda kukan da suke na zama na murna ne.
Da yake damka daliban, Kwamishinan yan sanda na jihar Kaduna Umar Muri ya ce wannan ceto daliban da aka yi, ya biyo bayan namijin ƙoƙarin gwamnati ne da kuma jami’an yan sanda.
Daua daga cikin daliban Sarah Sunday ta ce lallai ta ce an sha Gwagwarmaya matuka kama daga ashariya, duka ko da yake babu cin zarafi.
Daga bisani ta ari bakin sauran yan uwanta daliban ta ci musu albasa inda ta ce sun yafe wa mutanen da suka yi garkuwa da su.