Kasar Indiya na ci gaba da shiga halin ha’ula’i sakamakon annobar Korona, inda ta hallaka mutane sama da dubu hudu a rana guda, yayin ake ci gaba da kakaba dokar kulle a Jihohin kasar don rage bazuwar annobar.
Adadin Mutane dubu huɗu da dari daya da tamanin da bakwai da suka yi bankwana a duniya sakamakon, ya sa a yanzu haka kasar na da mutane dubu dari biyu da talatin da takwas da dari biyu da saba’in da suka mutu yun bayan barkewar wannan bala’i.
Kuma biss ga dukkan alamu wannan jarabawa ba nan kadai za ta tsaya ba, domin a halin da ake ciki kasar ta sake samun karin mutane sama da dubu arba’in da suka harbu da cutar adadin da ya sa ta gabda kamo kasar Amurka.
Masana da dama sun yi ta nuna shakku bisa adadin da mahukunta ke bayarwa inda suka ce zagayowar cutar karo na zai ci gaba har karshen watan Mayun da muke ciki, inda suke ta kira ga gwamnati da ta dauki kwararan matakai a fadin kasar.
Shugaban yan adawar kadar Raul Gandhi ya ja hankalin gwamnatin Firaminista Narendra Modi da ta rufe lasar ruff, muddin ana son ganin bayan annobar.