Daga Abdullahi Kebbi.
Wata tankar mai tayi taho mu gama da Hightlander Jepp a jahar Ogun, inda tayi sanadiyar mutuwar mutum 1 sannan ta jikkata mutun 8.
Kwamandan kiyaye hatsari na jahar Ogun shine ya bayyanawa kamfanin dillancin labaru na najeriya hakan, Inda yace hatsarin ya fada ne kan mutum 9 sai dai mutum daya ya rigamu gidan gaskiya, sannan takwas sun jikkata.
Sai dai an bayyana babbar motar da ta farkawa karamar da cewa tana kan hanyar zuwa legas domin dakon mai.