- Mai tsaron ragar PSG Gianluigi Donnarumma ya tabbatar da cewa abokin wasansa Kylian Mbappe ba zai bar kungiyar ba
- Hakan ya biyo bayan wasu rahotannin da ke alakanta shi da komawa Real Madrid
- Mai tsaron ragar ya bayyana haka ne biyo bayan nasarar da PSG ta samu a Lens
Mai tsaron ragar Paris Saint-Germain Gianluigi Donnarumma ya tabbatar da cewa abokin wasansa Kylian Mbappe ba zai bar kungiyar ba a kakar wasa ta bana sakamakon rahotannin da ke alakanta shi da komawa Real Madrid.
Donnarumma ya bayyana haka ne biyo bayan nasarar da PSG ta samu a Lens a gasar Ligue 1 ranar Asabar.
KARANTA WANNAN: EPL: ‘Sakamako Marar Kyau’ – Piers Morgan Ya Zargi Arsenal Kan Kasa Doke Fulham
An danganta Mbappe da barin PSG zuwa Real Madrid a wannan kasuwar musayar ‘yan wasa.
Kwantiraginsa da PSG zai kare a bazara mai zuwa, kuma har yanzu bai kulla sabuwar yarjejeniya da Parisians ba.
Da yake magana da Free Ligue 1, dan wasan na Italiya ya ce: “Abin farin ciki ne a yi wasa da Kylian. Yana da ban mamaki. Zai zauna? Eh, na tabbata.”
A wani labarin kuma, EPL: Ku Ba Komai Ba Ne, Ba Ku Isa Yin Wasa a Kulob din Ba – Souness Ya Caccaki ‘Yan Wasan Man Utd
Tsohon dan wasan Liverpool, Graeme Souness ya caccaki ‘yan wasan Manchester United uku kan rawar da suka taka a kungiyar Red Devils
Tsohon dan wasan ya ce ’yan wasan uku su ba komai ba ne, kuma ba su isa su buga wa Man United wasa na dogon lokaci ba
Bana tunanin daya daga cikinsu ya isa ya zama dan wasan United na dogon lokaci kuma ya kai kulob din inda suke son zuwa a matsayin babbar gasar kwallon kafa ta duniya
Tsohon dan wasan Liverpool, Graeme Souness ya caccaki ‘yan wasan Manchester United uku Jadon Sancho, Antony da Alejandro Garnacho, kan rawar da suka taka a kungiyar Red Devils kawo yanzu a kakar wasa ta bana.
Souness ya ce Sancho, Antony da Garnacho ’yan wasa ne da ba komai ba, ya kara da cewa ba su isa su buga wa Man United wasa na dogon lokaci ba.