Jami’an Hukumar yaƙi da sha da hana fataucin muggan ƙwayoyi NDLEA ta yi nasarar cafke wani ɗan Afirka ta Kudu a babban filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake birnkn Tarayya Abuja.
NDLEA ta ce ta dafe matashin ne mai shekara 29 tare ɗauke da sinadarin haɗa muguwar ƙwaya mai haɗarin gaske a yunkurinsa na yin fasa kwaurinta zuwa gabashin Afirka.
Yayin wani binciken fasinjoji ne dai aka yi dacen yin na mujiya da shi a jirgin kamfanin Ethiopian Airlines dake kokarin tashi daga Abuja zuwa Addis Ababa na ƙasar Habasha.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwastam sun cafke wiwi da ya kai kimanin naira miliyan 170 a jihar Kebbi
Kakakin NDLEA din Femi Babafemi ya ce baya ga wannan sinadiri kazalika akwai wasu sinadaran na daban da aka samu cikin jakar kayansa wanda aka ƙullasu daban daban wadanda duk yana kokarin fasa kwaurinsu ne.
Babafemi ya ce binciken da suka gudanar ya tabbatar musu da cewa dan ƙasar Afirka ta Kudun mai suna Mista Jean-Pierre ya yi basaja ne ta inda ya tura kayan nasa ya yi gaba yayin da shi kuma ya sauka birnin Legas a ranar Asabar din 19 ga watan Agusta daga Abidjan na Cote d’Ivoire.
Daga nan ne kuma ya tashi zuwa Abuja a ransr talata inda ya saɓi jaka mai launin shuɗi dake ɗauke da waɗannan muggan sinadarai kafin daga bisani ya nufi filin jirgin na Nnamdi Azikiwe don ḍaukar hanya.
A wani labarin majiɓancin wannan kuma, hukumar ta NDLEA ta yi nasarar gano wata mota da aka yasar da ita a kan hanyar Darazo dake Jihar Gombe dauke da ƙwayoyi da suka kai 373,420 ciki har da ƙwayar tramol da kuma Diazepam.
Kazalika a Jihar Ogun ma dai haka zancen yake inda jami’an na NDLEA suka yi nasarar cafke wani dilar ƙwayoyi ɗauke da ƙwayar tramol kimanin 80,000.