Aƙalla mutane 14 sha huɗu ake kyautata zaton sun jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a marabar Magboro dake kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa motoci uku suka yi arangama yauin hatsarin inda motar farko ƙirar Mazda Bas ta yi taho mu gama da wata motar safa lamarin da ya sa makamabciyarta ta yi walankeluwa ta gamu da su baki daya.
Wani ganau ya shaida cewa motar mai launin rawaya ta yi mummunar wargajewa bayan Mazda Bas din ta yi arangama da ita.
KARANTA WANNAN LABARIN: NDLEA ta cafke ɗan Afirka ta Kudu da sinadarin haɗa muggan ƙwayoyi a Abuja
Wani matuƙi da ya tsallake rijiya da baya ya shaida cewa hukuncin Ubangiji ne kaɗai ya tseratar da shi amma da shi da fasinjar da sun taka sawun ɓarawo sakamakon hatsarin.
“Direban motar Mazda din yana gudu ne da ya wuce kima. Ya zo daga ya daki wata mota inda kuma mirgine zuwa wani makaifa ta marabar inda masu babura suke yawa zama”
“Hannun direban ya matukar rikicewa inda har ta kai ga ana ganin ƙasusuwa, lamarin ya yi muni matuƙa”
Wani ɗan acaɓa da ya bayyana sunansa da Ahmad ya bayyana yadda ya ga jami’an Hukumar kiyaye haɗɗura ta kasa FRSC ke tattara mutane inda ya ce yana kyautata zaton da dama daga cikinsu ma sun rigamu gidan gaskiya.
Sai dai da aka tuntuɓi kakakin Rundunar Florence Okpe ya musanta batun rasa rai inda ya ce mutane 21 ne suka gamu hatsarin yayin da 14 suka jikkata.