By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun ce Akalla mutane 15 ne suka mutu a wani hatsarin mota da aka yi a kauyen Duma dake karamar hukumar Edati dake jihar Neja yayin da a jihar Bauchi tsakanin ranar Lahadi zuwa jiya mutane shida suka mutu.
A hatsarin daya afku a jihar Neja dai tireloli biyu ne suka hadu da wata motar kasuwanci ta Sharon inda abin ya faru da misalin karfe 10 na safiyar jiya.Tirelolin guda biyu wanda daya ke dauke da alluna, daya kuma tana dauke da kayayyaki iri-iri wadanda suka hari Minna babban birnin jihar Neja.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Motar kasuwanci ta Sharon wacce aka ce tana dauke da fasinjoji, galibi ‘yan kasuwa dake kan hanyar zuwa kauyen Kudu domin cin kasuwar mako-mako, na cikin sauri, inda aka ce ta kutsa kai cikin tirelar ta bugeta kuma nan take ta kama da wuta.
Sauran tireloli biyu da wata mota guda sun kutsa cikin motocin da ke cin wuta inda suma suka kone kurmus.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa direban motar dake dauke da alluna ya samu raunuka kuma an garzaya da shi babban asibitin Kutigi.
Kwamandan sashin hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC a jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, yace mutane shida ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota daya afku a ranar Lahadi.Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a Bauchi jiya, yace wasu 15 sun samu munanan raunuka sakamakon wannan mumunan hatsari.
“Na yi bayanin cewa hatsarin ya rutsa da wata motar bas Toyota Hiace ta Kano Line, mai lamba KN21-H41 a kauyen Kwanan Digiza dake kan hanyar Jama’are zuwa Azare da misalin karfe 11:30 na safe.sannan yace mutane shidan da suka mutu dukkansu matane.
Kwamandan sashin, wanda ya bayyana cewa musabbabin hatsarin hatsarin ya faru ne a saka makon sauri, sannan yace mutane 21 ne hadarin ya rutsa da su, wadanda suka hada da maza hudu, mata 14, yaro namiji daya da yara mata biyu.