Rahotanni daga Jihar Legas, na ce Mutane a kalla 5 ne suka jikkata, sakamakon wata wuta da ta tashi, a makaranta koyon harkar Shari’a dake Victoria Island a Jihar.
Shaidun gani da Ido sun ce, Wutar ta tashi ne bisa zargin Wutar Lantarki da haddasa gobarar, da misalin karfe Goma na dare Jiya.
Jim kadan da tashin Wutar ne kuma sai jami’an tsaron makarantar suka hanzarta kashe dake rukunin dakunan daliban, Wanda anan ne Wutar ta tashi, kafin daga bisani jami’an kashe Gobara suka karasa wajen.
Mai magana da yawun Hukumar kashe Gobara a Jihar, Amodu Shuaaibu ya ce ba a samu rasa Rai ba yayin gobarar.