Mutane tara ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota wanda ya afku tsakanin jiya Asabar zuwa Yau Lahadi akan babbar hanyar Ibadan zuwa Iseyin.
Jami’in ilmantar da jama’a na hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC shiyar jihar Oyo, Mista Paul Okoduwa, ya tabbatar da adadin a ranar Lahadi.
Inda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Niggeria NAN cewa, mutane 25 ne hatsarin ya rutsa da su sakamakon gudun wuce kima da motocin sufuri guda biyu suka yi.
Okoduwa ya shaida wa NAN cewa, wadanda suka mutu sun hada da maza shida ne mata uku, yayin da maza tara da mata shida suka samu mummunan raunuka daban -daban.
KARANTA WANNAN. LABARIN: Wani Basarake a Taraba ya rasu a Fadarsa
“Mutum guda ne kawai bai samu rauni ba”, in ji shi.
Ya Kara da cewa hatsarin ya rutsane da Moto ci biyu kirar Mazda da kuma Toyota Hiace mai lamba BDJ 400 YK .
Kazalika ya ce, an ajiye gawar-wakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa a wani asibiti mai zaman kansa, yayin da wadanda suka samu raunuka ke jinya a asibitin Our Lady, Iseyin.
A karshe Okoduwa ya gargadi masu ababen hawa da su yi biyayya ga duk dokokin zirga -zirgar ababen hawa, da kuma yin tuki cikin iyakokin da aka amince da su..