A Kalla Mutane tara me suka gamu da ajalinsu a wani hatsari da ya auku a karamar hukumar Igeuben ta Jihar Edo yayin da wata tawagar yan biki ke dawowa daga kauyen Agbor zuwa Ewohimi.
To saidai Kwamandar Hukumar Kiyaye hadura ta kasa FRSC dake Jihar ya ce mutane biyar ne kawai suka rasa rayukansu yayin da aka garzaya da uku zuwa asibiti wur janjan, sai kuma biyu da suka tsallake rijiya da baya ba tare da ko kwarzani ba.
Mutanen dai suna Hanyar su ta zuwa Ewatto dake karamar hukumar Esan ta Kudu don halartar wani taron biki a garin.
Shi dai wannan hatsari ya auku ne sakamakon taho mu gama da motar Bas din yan bikin ta yo da wata Tirela.
Kwamandar Hukumar FRSC din ya ce hatsarin ya biyo bayan gudun wuce kima ne da direbobin motocin biyu ke yi