Yan kungiyar ISWAP sun kaddamar da wani mummunan hari a garin Rann, shelkwatar karamar hukumar Kala Balge dake jihar Borno.
A cewar wata majiya, mazauna garin sun tsere zuwa kasar Kamaru sanadiyar harin.
Garin Rann na da iyakan da kasar Kamaru ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kaduna ta Garkame Kasuwannin Mako-mako a Kananan hukumomi 5
Rahotanni sun nuna cewa, mayakan Kungiyar da yawan gaske, sun afka garin Rann ne da sanyin safiyar yau Litinin.
Sai dai haryanzu, ba’a Sami cikakken bayanai kan harin ba, ya yin da rahotanni ke nuna cewa, Maharan sun yi bata kashi da jami’an soji, bayan sun sanyawa gidajen mazauna garin wuta.
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaye sunan shi ya ce, fararan hula a garin da dama sun bar gidajen su.
Kazalika wani shaidan ya ce, Mayakan Kungiyar ISWAP sun farmaki garin ne kwanaki kadan, bayan an sanya Sojoji a garin.
A wani labari Kuma.
Wani jirgin yakin sojin Nigeria ya hallaka yan bindiga da dama, a wani ginin makaranta dake karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara a jiya Lahadi.
Jirgin ya kuma Kai samame ta sama a yankin Zangon Dammaka da Jajaye, inda shugaban yan bindiga Kachalla Haru da magoya bayan sa ke boye.
Wata majiya ta karkashin kasa ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na PRNigeria cewa, rundunar hadaka dake aiki a Zamfara ce ta jagoranci wannan samamen a karshen makon da ya gabata.
Shaidan ya bayyana cewa, ” A jiya Lahadi 29 ga watan Augustan shekarar 2021 da misalin karfe 2 na rana, Munsami wani sahihin bayani dake cewa, yan bindiga sama da 100 sun yi wa wani ginin makaranta kawanya a kwauyen Gidan Rijiya na garin Galadi, dake keramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara”
” Hakan yasa rundunar hadaka ta Operation Hadarin Daji, ta tada jirgin Saman sojin Nigeria domin Kai samame a yankin, inda hakan yasa akyi nasarar kashe wasu yan bindiga da dama, da kuma lalata musu makamai” inji shi
Kazalika jirgin Saman ya Kkai samame maboyar Halilu Tubali dake dajin Subulu.
Sai dai haryanzu ba’asan yawan yan bindigan da rundunar ta yi nasarar kashe wa ba, Amma shaidan ya ce, an kashe akalla guda 50 da kuma kone musu Babura a kyauyen Gidan Rijiya.
Sai dai kamfanin Dillancin labaran ya ce, ya yi kokarin ji ta bakin jami’in Hulda da jama’a na rundunar soji saman Nigeria Air Commodore Edward Gabwet, amma wayar shi ta ki shiga.
Comments 1