Rundunar hadaka data kunshi na sojin kasa, da kuma na Sojin Ruwa, a jiya Litinin, sun farmaki gungun barayin Mota a jihar Imo, inda nan take suka kashe uku daga cikin bata garin.
An Samar da rundunar ce daga bataliyar sojin kasa ta 34 dake Obinze, da kuma ta sojin Ruwa tawaga ta 211, inda aka bayyana cewa, sun sami nasarar ce, biyo bayan wani kiran waya daga al’umar karamar hukumar Nhor Okpala dake jihar ta Imo.
Kazalika majiyar jaridar Dimokuradiyya ta bayyana cewa, Rundunar hadakar sojin, ta farmaki barayin motocin ne a garin Umuonyenwere Umuow na karamar hukumar Nhor Okpala inda su ka yi musayan wuta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane da dama sun haura Kamaru, ya yin da yan ISWAP su ka Kai hari Borno
Kazalika nan take batagarin uku suka bakunci lahira, ya yin da rundunar ta yi nasarar kwace motar da suka sace.
Kwamandan Bataliya ta 34 dake Obinze Janaral Raymond Utasaha da takwarar shi I. Ayo, sun yaba wa al’umar garin bisa yadda suka basu bayanan gungun barayin akan lokaci.
Comments 1