Jama’a na ci gaa da komawa muhallin su a Kasar Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Congo bayan da dutse mai aman wuta ya tilasta musu tserewa daga gidajen nasu.
Wutar wacce ta yi sanadiyar ɓacewar yan uwan wasu mazauna yankin, ta sanya sararin samaniya yayi ja-wur inda kuma.
Tsaunin Nyiragono ma makwabtaka da birni Goma da adadin jama’arsa ya kai miliyan biyu ya yi ta fitar da tartsatsin wuta mai duwatsu ko da yake Allah Ya takaita shi kawai a birnin ne.
Kawo yanzu mutane goma sha biyar sun rasa rayukansu yayin ibtila’in, amma sai dai ana ganin adadin ka iya fin haa nan gaba yayin da jami’an ceto ke kara shiga wuri mai tsarkakiya da lamarin ya ritsa da shi.
Wani Jami’in Gwamnati Mai suna Patrick Muyaya ya tabbatar da cewa mutane tara cikin sha biyar din sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke hanyar tserewa, sai kuma huɗu daga cikin su ke kokarin guduwa daga gidan fursuna insa sauran biyun kuma wutar ce ta kona su kurmus.
Kimanin yara ƙanana 170 ne ake kyautata zaton sun ɓace ɓat, yayin da wasu karin 150 kuma suka yi bankwana da iyalansu.