Mutane Dubu 18,429 suka kamu da Cutar Hanta a Jahar Nasarawa
Aƙalla Mazauna Jihar Nasarawa 18,429 ne suka kamu da cutar Hanta rukunin Hepatitis B da C a faɗin ƙananan hukumomin 13.
Kwamishinan lafiya na jihar, Pharm. Ahmed Yahaya, wanda ya yi magana a madadin Gwamnatin Jihar ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da Manema Labarai a bikin ranar yaƙi da cutar Hanta ta Duniya na shekarar 2022 mai taken ‘ yanda cutar zata iya kama ka, a Lafia, Babban Birnin Jihar ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zulum yace Talauci na iya Tilastawa Ƴan gudun Hijira shiga Ta’addanci
Kalaman sa“Hukumar Lafiya ta Duniya ce ta keɓe ranar yaƙi da cutar Hanta ta duniya don gane cutar Hepatitis a matsayin ƙalubalen Kiwon Lafiyar Jama’a na duniya.
Ana gudanar da bikin ne a duk ranar 28 ga watan Yuli domin a ƙara ganin yadda cutar take da kuma samar da karin kuɗaɗe domin Yaƙar ta, tare da kawo dauki ga mutanen data kama, da nufin daƙile yaɗuwarta.