Wasu fusatattun mutane sun kona motoci biyu na hukumar hana fasa kwauri ta kasa reshen jihar Sokoto, domin nuna adawa da kashe mutane hudu a wani hatsarin mota da ya rutsa da motocin kasuwanci guda uku a jihar.
Mutanen sun zargi wani shingen binciken hukumar kwastam da ke Asara Unit a Illela da haddasa wani mummunan hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu.
Shedun gani da ido sun yi ikirarin cewa, -Biyu Toyota Avenses da Golf Salon ne suka yi karo da juna a lokacin da suke kokarin gujewa kamawa ta hanyar tsallake wani shingen bincike da jami’an Kwastam na kasa suka dora.
Majiya mai tushe ta ce direbobin da lamarin ya shafa, ana zarginsu da lodin motocinsu da haramtattun kayayyaki, kamar shinkafar kasar waje da man kayan lambu da kuma ganin shingen binciken da hukumar ta Kwastam ta yi, inda suka yi yunkurin kaucewa kamun, kuma a cikin haka ne suka haddasa asarar rayukan mutane hudu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.
An tabbatar da mutuwar mutane hudu a wurin da hatsarin ya afku yayin da wasu shida da suka samu raunuka aka garzaya da su wani asibiti da ke kusa da karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sokoto.
Majiyoyi sun ce ’yan bangar da suka fusata a kauyen sun mayar da martani game da hadarin inda suka fara kai farmaki kan kadarori da sauran cibiyoyi na Hukumar Kwastam, inda aka kona motocin Hukumar Kwastam.
Majiyoyi sun ce an dauki lokaci a lokacin da sojojin Najeriya suka shiga tsakani domin dakatar da kai hare-hare kan cibiyoyin hukumar kwastam ta Najeriya da ke cikin sashin.
Kakakin Hukumar Kwastam ta Sokoto da Zamfara na Hukumar Kwastam Tahir Balarabe ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ya tabbatar da cewa wasu fusatattun mutane sun kone motoci biyu na rundunar da daya na jami’in da ke kula da sashin.
Mista Balarabe ya ci gaba da cewa jami’an na gudanar da ayyukansu ne kawai ta hanyar hana shigo da haramtattun kayayyaki cikin kasar nan kamar yadda dokar hukumar kwastam ta tanada.
Comments 1