A wata firarsa da BBC hausa Sanatan kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya Sanata malam Uba Sani Yace a yanzu ba Lokacin nuna inda aka dosa bane a bangaren Siyasa sai Hukamar Zaben Mai Zaman kanta INEC ta Hura usur din Siyasa kafin nan sai kowa ya bayyana inda ya dosa, Malam Uba Sani ya Fadi Hakan ne Acikin bidiyon da BBC ta fitar da safiyar yau a shafinta Facebook an hango ana tambayar Sanatan da Cewa…
BBC: Wanne mataki kuke ‘dauka a majalisa da Kare darajar Naira?
San Uba: Kamar yadda na ‘fada ita wannan Matsala kamar yadda nake fa’da Abu biyu ya kawo shi akwai annobar COVID-19 Wanda shi Karan kanshi ya tabba Tattalin Arzikin ko Wacce Kasa Dake duniya ba iya Nageriya ba, Kuma akwai wannan Matsalar na Rashin tsaro Wanda shima ya addabi kasar kusan ko wanne bangare idan kaje zaka ga ana Samun Matsala ta Rashin tsaro manoma Basu noma Manyan Kwamfanunnukan mu na wannan kasa zaka samu ko dai suna gab da su mutu ko Kuma sun kamo Hanyar mutuwa zaka Samu Abu kankane Wanda Bai taka Kara ya Karya ba sai an shigo dashi daga kasar Burtaniya ko Amurka Germany harma da Wasu kasahen na Africa to wa ‘yan nan abubuwa sune suke Karya Tattalin Arzikin Kasa Kuma dole ne mu tsaya muga munyi Abinda ko Wacce Kasa takeyi a duniya wurin ganin cewa anbawa Kwamfanunnukan kasar nan dama su rinka sarrafa abubuwa domin idan an fita dashi kasar waje mu ma mu samu dala ta shigo nageriya.inji Sanatan.
BBC: me mukeyi Kan Matsalar tsaro?
Sen Uba: Maganar tsaro Abinda zamu iyayi a majalisar ‘daya ne kawai shine mu Kai Kudri Kuma Ni kaina na Kai kudri majalisa Kan tsaro sun Kai goma sha’daya Kuma nasan abokan aiki na ma tunda muka Shiga wannan majalisar ta tara munyi Kudri ya kai samada ‘dari bani ka’dai ba akwai abokan aikina Wanda Suma sunyi Kudri kala-kala. Akan Maganar tsaro a wannan kasa Kuma shi kundin tsarin mulkin Kasa kullum Abin da muke magana akai shine a ƙirƙiro ‘yan Sanda na jihohi domin idan ba’ayi Haka ba Matsalar tsaro ba zai Kare ba.
BBC: bangaren zartarwa ya aikin da shawarwarinku kenan?
Sen Uba: Kamar yadda ka sani mun bayarda shawarwari da dama a yanzu Zan iya ce maka akwai shawarar da muka bayar a yanzu ne ma ake aiki da ita mun fa’di Cewa Sojojin sama suyi anfani da ‘yan Sanda da Sojojin kasa su zauna dasu aje abi Mutanen nan da na’urori na duniya domin komai ya chanja inda za’aje a duba su ta sama ai musu ruwan bama-bamai mutanen Nan kowa ya sani daji kan da suke anfani dasu ba wai yayi nisa da gari bane ba ana maganar Boko Haram ba ne da suke dajin Sambisa a wannan Lokacin amma ana Maganar ‘yan ta’addan kauyukan ma da suke Ciki Bai wuce kilo mita hu’du Zuwa biyar ba da Cikin Gari.
BBC: Menene ya banbanta ‘yan Sandan jihar da ‘yan banga?
Sen Uba: Ina ‘yan Banga Suka Sami hurumi da damar rike Bindiga? Kuma wa zai sa su rike Bindiga ‘din? Ba kowa bane za’a bashi Bindiga kuma ace yayi Abinda ya kamata Yayi da ita shiyasa muka ce a kawo ‘yan Sandan jiha domin Yan Sandan jiha Zan fa’da maka banbancin su da ‘yan Banga, domin Yan Banga ba zasu Sami lasisin rike Bindiga ba Irin su AK47 wa yanda irin Wacce Yan ta’addan suke anfani dasu ba zaka ce ‘dan Banga yaje ya tunkari ‘yan ta’adda Wanda ke rike da AK47 Kai Kuma ka tafi da gora ko Kuma da bindingar toka ba zai yuwu ba.
BBC: ance Kaine magajin El’rufa’i a 2023 yaushe zaka fito?
Sen Uba: Ina da kyakkyawar alaka da Kuma Tarayya da Mai girma Gwamna Sabo da Haka duk Lokacin da muka zauna muka yanke hukunci ga Abinda mukaga shine zai fi ma jihar kaduna kawo mata Cigaba a Lokacin Nan zamu gayawa mutanenmu ga inda muka dosa Amma Yanzu Abinda ke gabana shine kamar yadda ka sani Ina rike kwamiti ne Wanda kusan a kasar nan shine yake da Ayyuka da dama domin duk Abinda ya shafi bankuna da inshora da duk Sauran harkokin kasafin kudi na kasar nan Yana wannan kwamitin nawa Sabo da Haka ni a ganina idan an baka aiki sai ka Gama Wanda aka baka idan kayi kokari Abinda kayi Al’umma suka ga Abinda kayi su Kuma sai su fito su duba cancantarka Amma Yanzu Ni nafi Mika karfina da Lokaci na ga wannan aiki da aka zabeni na Sanata Amma Duk masu maganganun nan suna Mana fatan alkhari suna Cikakken ‘yancin Yi Kuma suna da damar da zasuyi.
BBC: bikin Magaji baya Hana na magajiya!
Sen Uba: ita harkar Siyasa da harkar Gwamnati idan bakayi Sa’a ba ka bar Aikin dake gabanka kaje ka raja’a a kan wani Abu to sai ka manta da Aikin da aka baka Amma idan Lokaci yayi aka busa usur akace gashi INEC ta fito Wanda itace zata Bayarda huri min fita a Fara Maganar takara to a wannan Lokaci in Allah ya yarda zamu fito mu fa’da wa Mutane inda muka dosa.
BBC: Yaya kake kallon makomar APC a jihar kaduna a zaben 2023?
Sen Uba: A Tarihin jihar kaduna karkaf ba’a taba samun Gwamnan da yazo yayi aiki irin Gwamna Malam Nasiru El Rufa’i ba.
BBC: meyasa yake Shan suka?
Sen Uba: Lokacin da yake aiki amatsayin shi na minista kusan kowa dake Abuja Yana ta kukan Cewa yazo Yana ta abubauwa Jama’a suna kuka Amma Bayan ya tafi da Shekaru biyu Zuwa uku kowa sai ya Fara Cewa Ina Malam Ahmad El’rufa’i yake Muna so ya dawo abuja ta lalace to mutun ne Wanda Indan yazo yanayin Abinda wani ba zai iyayi ba, Kuma ni Abinda na duba na gani shine ne shi ba’a kwaikwayon sa Bai zai yuwuba kace zaka kwaikwaye shi ba don mutun ne yazo yayi Gwamnati domin yayiwa Mutane aiki Bai bukatar a yabe shi Yana so inya Gama aikin ne Jama’a su duba suga me yayi shiyasa yanzu Duk masu kuka a Kaduna Nan da Shekaru kadan zasuyi kukan Cewa Ina Mai girma Gwamna yake Malam Nasir Ahmad El’rufa’i domin Abinda yakeyi a kaduna Tarihi yake kirkirowa ko yake kafa wa.
BBC: Amma Wasu na zargin Gwamnatinsa da Rashin adalci ga kudancin Kaduna?
Sen Uba: to ni Ina Ganin wannan Abu ne kawai irin na Mutane ‘yan Siyasa domin sai ka duba ka ga babu wani bangare a jihar kaduna da ba’a yin Ayyuka yanzu kaje kafancan kaga Ayyukan da ake a Zaria irinsa akeyi a kafancan shi kuma ake a kaduna in ka duba sai kaga ko wanne bangare na jihar kaduna ba inda Mai girma Gwamna Bai je ba yayi masu tituna ya gyara Makarantu yayi asibitoci Kuma ni Ina Ganin wannan shine Cigaba Amma Mutane sun Saba da Siyasa na da can da zaka zo ka zagi Gwamnati ko ka Bata Gwamnati a Kira ka a baka Ku’di ko a Kira ka a lallabe ka to shi Kuma Mai girma Gwamna ba zaiyi Haka ba Bai Kuma Saba yin Haka ba, to don haka maganar Cewa Bai kyautatawa wani bangare a jihar kaduna Ni Ina Ganin Tsirarin Mutane ne Wanda Daman sun Saba su fito suyi batanci domin a biya su don suna anfani da wani bangare domin su biyama kansu bukata Amma ainihin mutanen jihar kaduna ga ba ‘daya ko mutanen kudanci ko mutanen Arewacin kaduna ko musilmai ne ko Kirista ne kowa na Tabbata indai ba zai kawo Siyasa ba to zai gamsu da Abinda Malam Nasiru Ahmad El’rufa’i yakeyi a Jihar Kaduna. Inji Sanata Uba Sani.
Comments 1