Cibiyar dake lura da dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC sun ce an samu karin mutane 176 da suka harbu da cutar Korona a cikin sa’oi 24 da suka gabata, abin da ya kawo adadin jama’ar kasar da suka harbu zuwa 5,621, kuma 176 sun mutu, yayin da mutum 1472 suka warke.
NCDC sun ce a jiya kawai an samu mutum 176 da ba suke dauke da cutar, wanda suka fito daga jihohi sha uku na Nijeriya wanda ya hada da; 95 a Legas, 31 a Oyo, sai kuma Abuja, inda aka samu karin mutane 11.
Sauran jihohin sun hada da Borno da Neja masu karin mutane 8-8, sai Jigawa mutane 6, a Kaduna kuma mutane 4. Jihar Anambra ke biye bayan samun karin 3, sai jihohin Nasarawa, Ribas, da Bauchi, yayin da Zamfara da Binuwe ke da mutum guda-guda.
Jihar Legas ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka harbu da cutar a jumlace, inda take da 2,373, sai Kano mai 761, sai Abuja mai mutane 397, Katsina na da 239, Borno da Bauchi na da 212 kowacce, sai Jigawa mai 197.