Akalla mutane 8 suka mutu, sakamakon wani hari da aka kai a garin Yelewta dake karamar hukumar Guma na jihar Benue.
Sai dun gani da Ido sun bayyana cewa, an Kai harin ne yayin da yan kasuwa ke kokarin rufe shagunan su.
Shugaban karamar hukumar Guma Caleb Aba ya bayyana wa manema labarai ta wayar salula a garin Makurdi cewa, an kashe mutane a harin.
Aba ya ce, an kai harin ne a kasuwar Yelewta, inda suka kashe mutane 8, lokacin da yan kasuwa ke kokarin rufe shagunan su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnonin PDP za su yi Taro, don tattauna rikicin cikin gida
Shugaban karamar hukumar ya kuma ce, tuni aka kai wadanda suka sami raunika asibiti, domin duba lafiyar su.
Anata bangaren jami’ar hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar DSP Catherine Anene ta tabbatar da harin, Amma ta ce, mutane 6 ne yan bindigan suka kashe sanadiyar harin.
Ta kara da cewa, “Jiya 24 ga watan Agustan shekarar 2021, da musalin karfe 7:45 na yammaci, rundunar yan sanda ta sami bayanan cewa, wasu yan bindiga da ba’asan ko suwaye ba, sun afka yankin Yelwata, inda suka kaiwa wani yanki da ke kusa daji hari.” Inji ta.
Comments 1