Biyo bayan rikicin shugabanci da ake Samu a Jam’iyar adawa ta PDP, Gwamnonin da aka zabesu a inuwar jam’iyar, za su yi wata ganawa a gobe Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.
Taron na gaggawa zai gudana ne karkashin jagorancin Shugaban kungiyar gwaunonin jam’iyar PDP, kuma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal. Bayan ji ta bakin takwarorin shi, a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun Daraktar Janar na kungiyar Honorabul C.I.D Maduabum.
Makwanni biyu kenan bayan gwamnan ya gana da kwamitin amintattu na jam’iyar, domin magance matsalar rikice-rikicen Shugabancin jam’iyar. Bayan wani sabon rikicin da ya balle a jam’iyar sakamakon Kotu ta haramta wa Shugaban jam’iyar na kasa Prince Uche Secondus daga ai’yana kanshi amastayin Shugaban jam’iyar na kasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Mutane da dama a Fulato
Hakan ya janyo jiga-jigan jam’iyar biyu Yemi Akinwonmi daga yankin Kudu, da Sanata Suleiman Nazif daga Arewacin Kasar nan, nuna bukatar su na neman Shugabancin jam’iyar.
Har’ilayau sanarwar ta ce, ” shugaban kungiyar Gwamnonin PDP kuma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal CFR, tare tuntubar takwarorin shi, sun shirya wani zaman gaggawa da zai gudana a ranar Alhamis 26 ga watan Augustan shekarar 2021, da musalin karfe 5 na yammaci.”
“Taron zai tattuna sabbin batutuwan jam’iyar ta PDP” inji sanarwar.
Kazalika “kungiyar Gwamnonin na bukatar dukkannin mambobin jam’iyar, da kuma masu ruwa da tsaki da su ci gaba da hakuri, a yunkurin kungiyar na ganin ci gaban jam’iyar”